Babban Limamin Masallacin kasa na Abuja, Dakta Muhammad Kabir Adam, a ranar Juma’a, ya yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su bayyana maboyar ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun da ke addabar kasar ga sojoji.
Wannan a cewar malamin, zai taimaka wa dakarun sojojin kasar da sauran jami’an tsaro da ke yaki da kalubalen tsaro a fadin kasar domin gaggauta daukar matakin kawo karshen matsalar da kasar ke fuskanta.
Dr Adam ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai, jim kadan bayan kammala sallar Juma’a domin tunawa da ranar tunawa da sojojin kasar ta shekarar 2022.
A cewarsa, zai yi wuya ‘yan Najeriya su bayyana maboyar makiya da ke dagula zaman lafiyar kasar, amma ya zama wajibi idan aka yi la’akari da kashe-kashen yau da kullum a kasar.
Dokta Adam ya bayyana cewa an gudanar da Sallar Juma’a ne a wajan, domin tunawa da jaruman Najeriya da suka mutu da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare martabar ikokin kasar nan, tare da tabbatar da zaman lafiya ya dawo kasa Najeriya.