Wani bala’i ya sake afkuwa a cocin Katolika ta Abakaliki, jihar Ebonyi inda Limamin cocin Rev. Fr. Raymond Eselu, ya mutu a kan tuƙi yayin da yake dawowa daga bikin jana’izar abokin aikinsa.
A cewar wata sanarwa da shugaban cocin Diocesan, Fr. Matthew Uzoma Opoke, ya fitar yace Eselu ya rasu ne a asibitin koyarwa na tarayya na Alex Ekweme, AE FETHA II, bayan wani hatsarin mota da ya afku a gaban babban cocin St.Theresa’s Cathedral dake Abakaliki.
KARANTA WANNAN LABARIN: A Kwai Kimanin Sama Da Bindigogi Miliyan 6 A Hannun Fararen Hula – Rahoto
Eselu, mai shekaru 47, ya halarci bikin jana’izar limamin cocin, St Paul’s Parish Amudo, dake karamar hukumar Ezza, Fr Christopher Agwu, wanda ya rasu a ranar 4 ga watan Agusta, bayan ya yi fama da rashin lafiya.
An tattaro cewa Eselu ya bar taron yana tuka motar sa ne domin zuwa ganin likitansa inda akan hanyar sa motar tai ta dungure wanda ta tsaya ba zato ba tsammani. An nada Agwu da Eselu a ranar 6 ga watan Yulin shekarar 1996, da 7 ga watan Yulin shekarar 2007, bi da bi.
Diocese wadda ta yi wa Agwu godiya a wajen binne shi, wanda Bishop na cocin, Mai girma Rabaran Peter Nworie Chukwu, ya jagoranta, ya bayyana Eselu, a matsayin hazikin limamin hamshakiyar raha, mai kwazo da aiki, wanda ya ji dadin murnar bikin taro.
Za a yi jana’izar shi a ranar 6 ga watan Satumba bayan kammala taro.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Beni Mai Hawa 7 Ya Danne Mutane A Legas
Wani gini beni mai hawa bakwai da ake ginawa a kan titin Oba Idowu Oniru dake jihar Legas, ya ruguje inda mutane kusan shida suka makale.
Babban Sakatare na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya tabbatar da faruwar lamarin a safiyar Lahadi.