Limamin Babban Masallacin Juma’a na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, Malam Abubakar Musa ya rasu. Rahotanni sun tabbatar da cewa shi ne Limami mafi dadewa a Arewacin Nijeriya.
Majiyar iyalinsa sun tabbatar da cewa ya rasu ne a ranar Lahadi 19 ga watan Janairun 2020, kuma tuni aka bizne shi a Samarun Zariya bayan sallar Isha’i kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Tsohon Marigayin, Sardunan Sakkwato, kuma tsohon Firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello shi ne ya nada Limanin. Ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 40, tare da jikoki sama da 100.
An bayyana cewa ya rasu yana da shekara 110 a duniya.