Kyaftin din Argentina, Lionel Messi, a ranar Asabar da daddare, ya kamo tarihin da gwarzon dan wasan kwallon kafa, Diego Maradona ya kafa na cin kwallaye takwas a Albiceleste.
Messi ya samu nasarar ne bayan ya zura kwallo a raga a gasar cin kofin duniya da Argentina ta doke Mexico da ci 2-0.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Yanke Wa Mutumin da Aka Kama da Katin Zabe Sama da 100 Hukunci a Sokoto
Kwallaye biyu da Messi da Enzo Fernandez suka ci ne suka baiwa Argentina nasara akan Mexico.
Kwallon da Messi ya ci Mexico a filin wasa na Lusail ita ce ta biyu a gasar.
Dan wasan mai shekaru 35 ya lashe kyautar gwarzon dan wasa a wasan da suka fafata a jiya.
Sai dai kwallon da Messi ya zura a ragar Mexico ta zama an Takwas jummula da ya ci a gasar cin kofin duniya zuwa takwas, inda ya yi daidai da tarihin Maradona na Argentina.
Dan wasan gaba na Paris Saint-Germain yanzu zai yi fatan ya zarce kwallayen Maradona lokacin da Argentina za ta kara da Poland a wasansu na gaba a gasar cin kofin duniya ranar Laraba.
A wani labari kuma, Gwamnan Arewa Ya Tsallake Rijiya da Baya Yayin da Babbar Mota Ta Murƙushe Motocinsa 2
Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya tsallake rijiya da baya bayan da wata babbar mota ta murkushe wasu ayarin motocinsa biyu a ranar Asabar.
A cewar wani ganau, lamarin ya faru ne jim kadan bayan gwamnan da wasu kwamishinonin sa suka shiga wata bas kirar Mercedes a karshen wani daurin aure a masallacin Agga da ke unguwar Dougirei highbrow a Yola, babban birnin jihar