Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta shirya gabatar wa da mai tsaron bayanta, Dejan Lovren damar sabunta kwantiraginsa da kungiyar domin ci gaba da zama zuwa karshen kakar wasa ta 2022 kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Wasu bayanai sun nuna cewa wata Kungiyar Zenith St Petersburg dake Rasha na son yin zawarcin dan wasan amma har yanzu ba ta tuntubi Liverpool ba sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa wakilin dan wasan ya fara magana da wasu kungiyoyin da suke bibiyar dan wasan.
Lovren dai yana da shekara 31 a duniya, kuma dan kasar Croatia. Ya koma Liverpool ne daga Southampton a shekarar 2014 a Fam miliyan 20.
Sannan tun bayan komawarsa ya taimaka wa Liverpool ta ci gasar Firimiyar Ingila na bana, bayan da ya buga mata wasanni 10 a kakar shekarar nan. Sannan ya bugawa Liverpool wasanni 131 a Firimiya, ya ci kwallo biyar, ya kuma lashe gasar zakarun Turai a 2019.