A daren jiya ta tabbata ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta cimma wani gagarumin tarihi a gasar zakarun nahiyar turai a wasan data fafata wato wasan rukuni kenan inda kuma ta sami nasara a wasan.
A jiyan dai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta cimma tarihin jefa adadin ƙwallaye 10,000 tunda aka kafa ƙungiyar wato tun lokacin data fara fafata wasan ƙwallon ƙafa kenan.
A jiyan dai ƙwallon da Diego Jota ya jefa ta farko bayan an dawo daga hutun rabin lokaci itace cikon ƙwallo ta 10,000 a tarihin Liverpool. Sakamakon wannan nasara da Liverpool tayi yasa itace take jagorantar rukunin da maki 6 daga wasanni 2 data fafata.
Liverpool dai itace tafi lashe gasar zakarun nahiyar turai a dukkanin ƙungiyiyin ƙwallon ƙafan da suke wakiltar ƙasar Ingila a gasar zakarun nahiyar turai, inda a yanzu tana da kofin har guda 6.
Liverpool dai ta kafa wannan tarihinne a ƙarƙashin jagorancin mai horas wa Jurgen Klopp wanda shine ya farfaɗo da karsashin ƙungiyar a ‘yan shekarunnan biyo bayan dogon suman datayi a shekarun baya.