Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta fitar da sunan Virgil van Dijk daga jerin sunayen ‘yan wasan da zasu fafatama gasar ajin firimiya ta ƙasar Ingila wato kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 biyo bayan mummunan raunin daya samu a wasan mako na 5 na gasar Firimiya.
Mai tsaron gidan Everton wato Pickford da van Dijk dai sunyi arangama ana tsaka da fafata wasan mako na 5 na gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila wasan da aka tashi kunnen doki wato 2 – 2 a ranar Asabar ɗin data gabata tsakanin Everton da Liverpool, inda wasan shine na farko da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton ta rasa maki bayan data lashe wasannin ta guda 4 a baya inda take jan ragamar teburin gasar da maki 13.
Sakamakon wannan mummunan rauni da shahararren ɗan wasan bayan na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ya tafi, ya sanya zai kwashe kakar wasa guda yana jinya wato kakar wasa ta 2020 zuwa 2021. A labaran da suke fitowa a wannan dare na Laraba an cire sunan Virgil van Dijk daga jerin sunayen ‘yan wasan dazasu ci gaba da bugawa Liverpool gasar ajin Firimiya ta bana.
Idan ba a manta ba daman tsakanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan guda biyu wato Liverpool da Everton akwai hamayyar cikin gida mai zafi sosai ganin yadda suke hamayya da juna tun a tarihinsu. Everton da Liverpool dai da a fili ɗaya suke fafata wasanninsu a shekaru da dama da suka gabata amma kuma rigimar hamayya mai taken Mesy Side Derby tasa kowacce ta kama gabanta.
Virgil van Dijk dai ya zo ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Southampton a shekarar 2018 inda ya zuwa yanzu ya buga wasanni guda 95 a Liverpool inda ya sami nasarar jefa ƙwallaye guda 10 a iya kusan tsawon shekaru uku daya kwashe tare da Liverpool.
A yanzu haka van Dijk zaiyi zaman jinya harta tsawon shekara 1 inda bayan ya warke zaici gaba da zama a Liverpool har kwantaraginsa ta ƙare.