Da ranar yau Asabar ne kungiyar Liverpool suka lallasa Newcastle da ci 3 da 1 a ci gaba da gasar Firimiyar Ingila da ake fafatawa a mako na biyar da fara gasar kakar wasa ta bana 2019/2020.
Willems ne ya fara ci wa Newcastle a minti na 7. Inda Mane na Liverpool ya rama a minti na 28, ya sake karawa a minti na 40. Sannan Muhammad Salah ya kara ta zama uku wanda hakan ya sanya aka tashi da ci uku da 1.