Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool kuma zakarun gasar ajin Firimiyar ƙasar Ingila ta sayi ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich kuma ɗan asalin ƙasar Andalus wato Thiago Alcantara awannan yammaci na Juma’a.
Tun a watannin baya ƙungiyar ta Liverpool ta nuna sha’awarta ta sayen sa amma abin yaci tura, sai dai za a iya cewa ta faru ta ƙare an yiwa mai dami zane ɗaya sata domin kuwa ta tabbata Alcantara ya zama ɗan wasan Liverpool.
Liverpool dai ta saye shi akan kuɗi £25m kuma ɗan wasan ya sanya hannu harna tsawon shekaru huɗu tare da Liverpool wato daga yanzu har zuwa 2024 kenan.
Alcantara dai ya taimakawa Bayern Munich ta lashe gasar zakarun nahiyar turai a kakar wasa ta bana inda ya nuna bajinta sosai sannan kuma ya lashe gasar Bundes Liga da dama da sauran wasu kofunan.
Shidai Alcantara ya taso ne tun farko a ƙaramar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona sannan kuma ya koma can ƙasar Jamus wato Bayern Munich lokacin Pep Guardiola yana can yasa aka sayoshi.