Liverpool ta sha da kyar a hannun Red Bull Salsburg a daren Laraba a kokarin da ta ke na kare kambunta a gasar zakarun nahiyar Turai a gidanta Anfield. Tun da farko sai da Liverpool din ta antaya wa bakin na ta kwallaye uku a raga amma suka dage, har suka farke dukkannin kwallayen, wasa ya zama 3-3 kafin daga bisani Mohamed Salah ya jefa kwallo daya a ragar Salsburg bayan an dawo hutu.
Liverpool dai ta yi rashin nasara a wasan ta na farko a gasar ta bana a rukuni na 5 sakamakon doke ta da Napoli ta yi, amma ta yunkuro a wannan wasa bayan tsohon dan wasan Salsburg da ke mata wasa a halin yanzu, wato Sadio Mane, ya fara saka kwallo a cikin minti 10 da fara wasan na jiya Laraba, Andrew Robertson ya ci kwallo ta 2, yayin da Mohamed Salah ya ci ta 3 da ta 4 wasa ya tashi 4-3.
Salsburg ta nuna wa Liverpool cewa ba kanwan lasa take ba, saboda a wannan kaka kawai ta ci kwallaye 40 a wasanni 9, saboda haka ta farke wadannan kwallaye cikin ruwan sanyi.