Firaministar Burtaniya, Liz Truss, ta nada Kemi Badenoch a matsayin mamba a tawagarta a wani sauyi a majalisar ministocinta bayan da Truss ta karbi mukamin a ranar Talata.
Wani sakon da aka wallafa a shafinta na Twitter mai inganci, na Firaministar Burtaniya, @10DowningStreet, a ranar Talata, ya bayyana cewa an nada Badenoch a matsayin Sakatariyar Harkokin Kasuwancin Kasa da Kasa kuma Shugabar Hukumar Kasuwanci.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: ‘Yan Takarar Gwamna 17 Na PDP Suna Ganawar Sirri Da Wike
Sanarwar ta ce, “An nada Kemi Badenoch MP @KemiBadenoch Sakatariyar Harkokin Ciniki ta Kasa da Kasa kuma Shugabar Hukumar Kasuwanci @TradeGovUK
Garanbawul Na Majalisar Ministoci
Sauran wadanda aka dana a ranar Talata wanda kuma Sarauniya Elizabeth ta II ta amince da su, kamar yadda ke ƙunshe a cikin sanarwar manema labarai ta 10Downing Street sun haɗa da:
Rt Hon Dr Thérèse Coffey, a matsayin Sakataren Ma’aikatar Lafiya da Kula da Jama’a. Haka kuma za ta zama mataimakiyar Firaminista.
- Rt Hon Kwasi Kwarteng, a matsayin Chancellor of Exchequer
- Rt Hon James Cleverly MP a matsayin Sakataren Harkokin Wajen commonwealth da Harkokin Ci Gaba
- Rt Hon Suella Braverman QC MP a matsayin Sakatariyar Gwamnati na Ma’aikatar Cikin Gida
- Wendy Morton MP a matsayin Sakataren Majalisar Dokoki da Baitulmali ( bulaliyar majalissa).wanda kuma zata halarci majalisar ministoci
- An sake nada dan majalisar Rt Hon Ben Wallace a matsayin sakataren tsaron kasa
- Rt Hon Brandon Lewis MP CBE a matsayin shugaban alkalai, kuma Sakataren Gwamnati na Shari’a
- Rt Hon Nadhim Zahawi dan majalisa a matsayin shugabar Duchy of Lancaster, ministan hulda da gwamnatoci da kuma ministan daidaito
- Rt Hon Penny Mordaunt MP a matsayin Shugaban Majalisar, kuma Jagoran Majalisa
Rt Hon Jake Berry MP a matsayin Minista ba tare da Fayil ba
- An sake nada dan majalisar Rt Hon Alok Sharma a matsayin Shugaban COP26
- Rt Hon Jacob Rees-Mogg MP a matsayin Sakataren Harkokin Kasuwanci, Makamashi da Dabarun Masana’antu
- Rt Hon. Simon Clarke dan majalisar wakilai a matsayin sakataren gwamnatin tarayya mai kula da inganta, gidaje da al’umma
- Kemi Badenoch MP a matsayin Sakatariyar Harkokin Kasuwancin Kasa da Kasa kuma Shugabar Hukumar Kasuwanci
- Chloe Smith MP a matsayin Sakataren Gwamnati na Ayyuka da Fansho
- Rt Hon Kit Malthouse MP a matsayin Sakataren Ilimi na Gwamnati
- Ranil Jayawardena dan majalisa a matsayin sakataren ma’aikatar muhalli, abinci da yankunan karkara
- Rt Hon Anne-Marie Trevelyan MP a matsayin Sakatariyar Harkokin Sufuri
- Rt Hon Michelle Donelan MP a matsayin sakatariyar harkokin zamani, al’adu, yada labarai da wasanni
- Rt Hon Chris Heaton-Harris MP a matsayin Sakataren Gwamnati na Arewacin Ireland
- An sake nada Rt Hon Alister Jack MP a matsayin Sakataren Gwamnati na Scotland
- An sake nada Rt Hon Sir Robert Buckland KBE QC MP a matsayin Sakataren Gwamnati na Wales
- Chris Philp MP a matsayin Babban Sakataren Baitulmali wanda zai halarci majalisar ministoci
A wani labarin kuma, Gwamna Zulum Ya Ziyarci Garin Bama, Wanda Ya Kasance Tungar ‘Yan Boko Haram
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a daren ranar Litinin, ya bayyana a babban asibitin garin Bama a wata ziyar bazata, domin sa ido kan yadda ayyukan kiwon lafiya ke kaiwa ga jama’a.
Ziyarar ba-zatan da Zulum ya kai asibitin da misalin karfe 10 na dare jim kadan bayan isowarsa garin Bama ta hanyar Maiduguri, kokarin duba lokaci da jajircewar ma’aikatan lafiya wanda ya zama dabi’arsa na kai ziyarar ba-zata da daddare zuwa manyan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko dake fadin jihar.