Ministan sadarwa da tattalin fasaha, Dr Isa Pantami, ya nemi da a daina dogaro da takardar shaidar kammala karatu wato Satifiket, a maimaikon haka a rika dogaro da kwarewa domin ci gaban bangaren tattalin arzikin fasahar zamani ta Nijeriya.
Dr Isa Pantami ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar na kammala karatu a Kwalejin horaswa ta Tsaro ta kasa a ranar Talata a birnin tarayya Abuja. Taken jawabinsa na sa shi ne; “Fasahar Tattalin arzikin zamani da ci gaban kasa a Nijeriya.”
Dr Isa Pantami ya jaddada cewa; sanin fasahar zamani da kuma kwarewa suna daga cikin ginshikan ci gaban bangaren tattalin arzikin fasahar zamani a Nijeriya tare da bin ka’idodin da aka shimfida na NDEPS.
Ministan har wala yau ya jaddada cewa ya kamata a rage lura da Satifiket wajen daukar aiki, inda ya nemi da a rika lura da me mutum ya iya idan har ana so kasarnan ta kamo kasashen da suka ci gaba. Ya lurantar da cewa mafi yawan kasashen da suka ci gaba wanda ya hada da Chana, Amurka, Morocco sun maida hankali akan abin da mutum ya koya ya iya fiye da Satifiket, inda ya ce yanzu da yawansu sun kafa cibiyoyin koyar da ayyuka.
Dr Isa Pantami ya ce satifiket na da amfani, amma shi ne abu na biyu da ya kamata a lura da shi. Inda ya ce abin da ya fi kamata a bai wa muhimmanci shi ne kwarewa da abin da mutum ya iya domin ci gabantar da bangaren kimiyya da fasahar zamani.