Jakadan Nijeriya a Benin, Janar Tukur Yusuf Buratai, yana ta kokarin ganin an dawo da Igboho da matarsa gida Najeriya. Kamar yadda Jaridar Punchnews ta wallafa a shafinta
Babban lauyan mai fafutukar kafa kasar Yarbawa Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bayyana irin mummunan halin da wanda ya ke karewa ke ciki a hannun Jami’an yan sandar Jamhuriyar Benin.
Shugaban lauyoyin, Yomi Aliyu ya bayyana hakan ne yayin da ya yi magana da jaridar The Punch a daren ranar Talata.
KARANTA:- Kungiyar mutan arewa ta ce Kama Nnamdi Kanu da Sunday Igboho ba shine mafita ba
A Jamhuriyar Benin aka tsare Igboho
Ya ce ƴan sandan na Jamhuriyar Benin sun kama Ropo, matar Sunday Igboho, sun ajiye ta a wani ɗakin ajiye wadanda ake zargi da laifi.
Ya ce: “Sun daure shi da mari a inda aka ajiye shi a Cotonou. Anyi hayaniya a filin tashin jiragen sama a lokacin da aka kama shi.
Sun buge shi a hannu sannan suka saka masa ankwa a hannun, yana cikin azaba kuma yana ta sharɓar kuka tamkar yaro ƙarami a lokacin da na kira shi, na ji shi.
Sun buge shi a hannu sannan suka saka masa ankwa a hannun, yana cikin azaba kuma yana ta sharɓar kuka tamkar yaro ƙarami a lokacin da na kira shi, na ji shi.
“Ita ma matarsa an saka ta a wani ɗaki daban amma ba a saka mata mari ba, ita ma matar tana kuka saboda yana cikin azaba.
Muna addu’ar kada su biya wani ya kashe shi., Ba daidai bane ka rufe mutum sannan ka saka masa mari.
“Kun san ya ji ciwo amma ba ku kai shi asibiti ba, mun ji cewar za a gurfanar da shi a kotu gobe ba mu san ko hakan zai yiwu ba.”
Idan za a iya tunawa dai an kama Igboho da matarsa ne a filin tashin jirage na Cadjehoun, Jamhuriyar Benin misalin ƙarfe 8 na daren ranar Litinin.
Suna shirin shiga jirgi zuwa Jamus kafin yan sandan kasa da kasa suka kama su.
Rahotanni sun ce jakadan Nigeria a Jamhuriyar Benin, Janar Tukur Yusuf Buratai yana kokarin ganin an dawo da Igboho da matarsa gida Najeriya.