Kasuwar hada-hadar sayen ‘yan wasa musamman a nahiyar turai kasuwa ce mai tsari da ake ware wani lokaci zuwa wani lokaci domin kowacce ƙungiya tayi ƙoƙarin taga tayi siyayya domin tunkarar kakar wasa ta bana da aka fara wato kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 inda tuni wasu ƙasashen sun shiga mako na biyar wasu kuma sun shiga mako na huɗu da fara fafata wasan.
Daga cikin siyayyar da wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan sukayi za a iya cewa wasu kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu inda wasu kuwa sun ɗakko amaryar da bata iya girki ba wato kwalliya bata biya kuɗin sabulu ba duba da yadda suka kashe manyan kuɗaɗe, sannan wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan kwata-kwata ba ‘yan wasan daya dace suka saya ba ganin cewar wasu matsalarsu ta ‘yan wasan tsakiya ce amma kuma sunje sun sayi ‘yan wasan baya, sannan kuma wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan matsalarsu ta masu horas wace amma kuma basu sayaba yayin da wasu kuma matsalarsu ta ‘yan wasan gaba ce amma basu saya ba.
A wannan rana ta Litinin wato 5 ga watan Oktoba na shekarar 2020 za a rufe hada-hadar kasuwar sayen ‘yan wasan a kewayen nahiyar ta turai, sai dai lokutan rufe hada-hadar kasuwar sayen ‘yan wasan ya bambanta a gasar rukuni-rukuni ta ƙasar Jamus wato Bundes Liga da gasar Premier ta ƙasar Ingila da gasar Laliga ta ƙasar Andalus da harma da gasar French League One ta ƙasar Faransa. Inda kowanne league lokacin rufe hada-hadar kasuwar sayen ‘yan wasan daban.
Ga jerin lokutan da za a rufe hada-hadar kasuwar sayen ‘yan wasan akowanne league:
1. Za a rufe hada-hadar kasuwar sayen ‘yan wasa a gasar Bundes Liga ta ƙasar Jamus a wannan rana ta Litinin da misalin ƙarfe 5:00 na yamma agogon Najeriya da Niger da Cameroon da kuma Chad, wato ƙarfe 4:00 dai-dai agogon GMT da Ghana.
2. A gasar Laliga ta ƙasar Andalus kuwa za a rufe hada-hadar kasuwar sayen ‘yan wasa da misalin ƙarfe 11:00 na dare agogon Najeriya.
3. Haka zalika a gasar League 1 ta ƙasar Faransa za a rufe hada-hadar kasuwar sayen ‘yan wasan da misalin ƙarfe 11:00 na daren wannan rana ta Litinin.
4. Itakuwa gasar Serea A ta ƙasar Italiya za a rufe hada-hadar kasuwar sayen ‘yan wasan da misalin ƙarfe 7:00 na daren wannan rana ta Litinin.
5. A ƙasar Ingila kuwa a gasar nan ta Firimiya za a rufe hada-hadar kasuwar sayen ‘yan wasanne dai-dai da yadda za a rufe na gasannin Laliga da French League One wato 11:00 da dare.
Sai dai dayake akwai sauran lokuta wato ‘yan awanni kenan kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa misamman wadda take da matsala tana da damar da zata iya zuwa tasayi ɗan wasan da takeso musamman a wajen dataga tana da matsala ganin yadda ake buga ƙwallo kuma har ƙananan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa sunyi gyara idan yanzu abin ya koma ƙaramar ƙungiyar ƙwallon ƙafa takan yiwa babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafa dukan kawo wuƙa.