Luis Suarez ya ci kwallo biyu a wasan da Barcelona ta taso daga baya ta yi nasara a fafatawar da ta yi da Inter Milan a Camp Nou a wasan zakarun nahiyar Turai a daren Laraba.
Inter ce ta fara cin kwallo ta hannun dan wasan ta Lautaro Martinez, har ma sai da ta kusan cin kwallo ta biyu amma mai tsaron ragar Barcelona Marc-Andre ter Stegen ya ceto ta, wasa ya ci gaba da zama 1-1.
Bayan nan ne Lionel Messi, wadda ya dawo daga jinyar da ya tafi, ya gyara wa Suarez wata kwallon, shi ko bai yi wata-wata ba ya jika wa Inter aiki.
Wadannan kwallaye dai da Suarez ya ci su ne kwallyensa biyu a gasar zakarun nahiyar Turai a fiye da shekaru 3.
Barcelona, wacce ba a doke ta a gida ba a wasanni 33 a gasar ta Turai, tana da maki 4, daidai da Borussia Dortmund, wadanda suka yi canjaras a wasan su na farko.