Ma’aikacin Gwamnati Zai Maido Da Albashi Na Shekara 11 Akan Takardun Bogi
Wata Babbar Kotun jiha da ke zamanta a Jos ta umurci wani babban ma’aikacin cibiyar binciken magungunan dabbobi ta kasa (NVRI), Vom, jihar Filato, Muhammed Nasiru, da ya mayar da albashin da ya karba na tsawon shekaru 11 a matsayin shugaban gudanarwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari yayi jawabi bayan Dangote, Hadiman sa, sun samu Lambar yabo mafi girma a Jamhuriyar Nijar
An kuma yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan yari saboda bayyana takardun karya da kuma rashin bayar da sahihin takardu wajen neman aiki na NVRI.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhume-tuhume biyu.
ICPC ta ce Nasiru bai cancanci daukar aikin ba, bisa la’akari da cewa hukumar kula da harkokin shari’a ta kasa (NJI), Abuja, ta yi masa ritayar dole ne a shekarar 2003.
Mai shari’a Christy Dabup, ya ba shi zabin tarar N150,000 a madadin zaman gidan yari.