An sako ma’aikatan karamar hukumar Zaria 9 cikin 11, da wasu Yan bindiga suka yi garkuwa dasu a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, bayan shafe kwanaki 19 a hannun su.
Matan tara da aka yi garkuwa da su, sun shaki iskar ‘yanci bayan an biya Naira miliyan 40 a matsayin kudin fansa.
Majiyoyin iyalan sun ce barayin na bukatar sabbin babura guda biyu, domin a sako sauran maza biyun suke ci gaba da rike su.
Da yake zantawa da wakilinmu, wani dan uwan daya daga cikin wadanda aka sako, ya ce tun da farko ‘yan bindigan sun nemi kudin, tare da sabbin babura guda biyu.
Sai dai majiyar ta ce barayin sun sako matan tare da ajiye mutanen 2, inda suka bukaci a kawo musu baburan.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa a farkon watan Nuwamba ne aka sace ma’aikatan karamar hukumar ta Zaria 11 a kauyen Idasu da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa ta’aziyya da daya daga cikin abokan aikinsu da ya rasa mahaifinsa.
Sakamakon katsewar hanyar sadarwa da aka yi a cikin yankin, ‘yan bindigar sun sako direban motar domin ya sanar da iyalan fasinjojin da suka yi garkuwa da su.
Ya zuwa yammacin ranar Asabar, wakilin Jaridar Daily Trust ya tattaro cewa matan tara da aka kai wani asibiti da ba a bayyana ba domin a duba lafiyarsu, har yanzu ba a sada su da iyalansu ba.
Comments 1