Sashen kula da lafiyar Ma’aikata na hukumar gudanarwar Ma’aikatan birnin tarayya Abuja ta fitar da wata takarda dake umartar ma’aikatan birnin tarayya Abuja da su mika kan su don a yi musu gwajin cutar Corona ta COVID-19.
Takardar ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan umarnin da Babban Sakataren Hukumar ya bayar ne biyo bayan wani taron hukumar gudanarwa da ya gudana a ranar 18/2/2021 kan cewa ko wani ma’aikaci da ya je a yi masa gwajin COVID-19.
Data tawagar Ma’aikatan lafiya na birnin tarayya Abuja ta yi cincirindo a Sakatariyar hukumar kula da ma’aikata ta birnin tarayyar daga ranar Litinin daya zuwa Juma’a biyar ga watan Maris din 2021.
Daga yanzu zuwa ko wani lokaci dai ana sa ran ma’aikatan za su fito don yin gwajin cutar ta corona da zarar an fadi ranar yin hakan