
- Ma’aikatan gwamanti sunfi Yan Siyasa cin Hanci cewar Yan Majalissu
- Yan Majalissun wakilai sun ce bincike ya nuna cewa a hanlin yanzu ma’aikatan gwamanti sunfi Yan Siyasa almundahana.
- Dan Majalissa Mathew N. Jagoran SPAC yake bayyana hakan lokacin da yake zantawa da jami’in Jaridar PUNCH a Abuja.
Yan Majalissun sune dai Wanda kundin mulki ya tabbatar a matsayin wakilai sun ce ” a hanlin yanzu suna kan bincike ne kan Shugaban Masu bincike na kasa tun daga 2015 zuwa 2018.
KARANTA:- Buhari ya nada sabbin sakatarori guda biyar na gwamnatin tarayya
Binciken zai ta’allaqa ne kan ministries da wadansu reshoshi na gwamnatin.
Uhoghide yace binciken dai kawo yanzu ya tabbatar da mafi munin inda ake almundahana shine wajan ma’aikatan gwamanti.
Yace “na Fadi hakan ne kan zargin da ake yi, zagaji mutane sukan ce suna korafi da Yan Siyasa sune sukafi yin cin Hanci.
“Mutane da dama sun aminta da cewa duk wani ta’adi da zai auku to ana dangata shi ne da Yan Siyasa, Wanda Kuma Yan Siyasar basu Kai kaso goma cikin sauran mutane ba”
“Binciken namu ya bayyana mana cewar mafiya yawan kudaden da ake sacewa ba Yan Siyasa ke sacewa ba.”
Yace “Mun bankado biliyoyin kudade da’aka sace daga asusun MDAs wadanda Yan Siyasa nawa ne keda irin wadannan makudan kudaden?”
“An Sha kawo mana karar satar kudade a bankin ma’aikatan gwamanti. Ba muna Kai karar maaikatu bane, yace ” babu tayadda za’a minista ya handame kudin batare da sanin mai kula da asusun ba.”
A yanzu dai SPAC tazo da sabbin tsarika Wanda zai tilastawa ma’aikatan dawo da kudaden da suka handame.
Yace ” Munu sami rahotanni da dama kan cinye kudaden Kuma mun gaya musu dasu gaggauta dawo dasu.
Yace ” Mun riga Mun yanke cewa duk Wanda ko wacce aka kama lokacin da yake jagoranci wani ma’aikata da zai fuskaci hukunci.
Yace ” duk maaikacin da aka gama da cin hanci shekaru goma baya za’a tun tubeshi ya bada bayani gamsashshen idan ba haka ba ya dawo da kudin ko Kuma ya fuskaci hukunci.
Yace ” yanda sa saci miliyan goma a shekarun baya ya isa yanzu ace yayi kasuwanci ya Sami ribar da zai biya”.
Comments 1