By Abbas Yakubu Yaura
A jihar Anambra, ma’aikatan gwamnati sun koma bakin aiki a sakatariyar jihar, yayin da aka bude wasu ofisoshin Ma’aikatan.
Da misalin karfe 1:00 na rana ma’aikatan sun fara komawa gidajensu da alama saboda rashin aiki a wuraren aikinsu.
A yau Litinin ne ma’aikatan gwamnati suka fara zuwa bakin aiki a jihar tun bayan da masu fafutukar kafa kasar Biafra suka bayar da wannan umarni a ranar 9 ga watan Agusta.
Duk da cewa kungiyar ta IPOB ta soke wannan umarni kafin ranar Litinin 15 ga watan Agusta, amma al’ummar yankin sun ci gaba da bin umarnin bisa ga dukkan alamu saboda tsoron sauran bangarorin kungiyar IPOB da suka sha alwashin ci gaba da aiwatar da dokar da aka soke zuwa yanzu.
A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar a kwanakin baya ta hannun kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a, C-Don Adinuba, ya bukaci al’ummar jihar wadanda suka hada da ma’aikatan gwamnati da su fara ayyukan zamantakewa da tattalin arziki a yau Litinin, inda ya bayyana cewa. kada a sake ranar Litinin a jihar a matsayin ranar da babu aiki.
Sai dai kuma an samu ingantuwar koma bayan harkokin kasuwanci a ranar Litinin a wasu sassan jihar. A Onitsha, Awka da Nnewi akasarin kasuwanni sun bude, duk da cewa ‘yan kasuwa da kwastomomi basu da yawa.
Wani dan kasuwa mai suna Celestine Ebili, wanda ya zanta da wakilinmu ya ce, “Mun bude a yau bisa umarnin shugabanninmu da jami’an gwamnati.
Haka kuma an sami gagarumin ci gaba a harkar sufuri, Ma’aikatan sufurin da har zuwa yanzu suka bi umarnin zama-a-gida, sun koma bakin aiki ranar Litinin yayin da wuraren ajiye motoci a jihar ke cigaba da zama a bude.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Wasu bankunan sun bude saboda abokan cinikin su , amma makarantun firamare da sakandare a jihar sun kasance a rufe.