Wasu ma’aikatan gwamnati a jihar Zamfara sun gudanar da sallah ta musamman a masallacin Idi da ke Gusau babban birnin jihar a ranar Asabar. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ma’aikatan da suka yi dandazo a masallacin da misalin karfe 10 na safe sun nemi daukin Ubangiji kan matsalar rashin samun albashinsu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Mummunar Gobara Ta Tashi A Wata Shahararriya Kasuwa A Jihar Oyo
Ma’aikatan dai sun ce an biya su albashi na karshe ne a watan Janairu, kuma suna fuskantar matsi wajen biyan bukatunsu.
“An matsa wa wasu daga cikin sun koma mabara, ba mu iya cin abinci ko sau daya a rana. Don haka, muka shirya wannan Sallah, wata hanya ce ta musamman don neman daukin Allah da ya bai wa mai girma gwamna, shugaban ma’aikata, ‘yan majalisar tarayya da duk wanda abin ya shafa, ikon tausaya mana.
“Mun sha wahala sosai saboda wannan gwagwarmaya, da yawa sun rasa rayukansu kuma muma ba ma son hakan ta same mi. Mun taru ne don neman taimakon Allah kan lamarin,” in ji daya daga cikinsu da ya nemi a sakaya sunansa.
Kokarin jin martanin gwamnatin jihar kafin hada wannan rahoto ya citira domin layin wayar kwamishinan yada labarai Ibrahim Dosara akashe take.
A kasa akwai hotunan ma’aikatan da suke gudanar da addu’o’i na musamman;
A wani labarin kuma, Ba Mu Da Masaniya Kan Sahalewa Emefiele Zuwa Hutu Don Karo Karatu –Fadar Shugaban Kasa
Fadar shugaban kasa ta ce ba ta da masaniya kan matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na bai wa gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele hutu domin yaje karatu. Kamar yadda Daily Trust Ta ruwaito.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Malam Garba Shehu, ne ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyin Daily a ranar Lahadi.