inec

Ma’aikatan INEC Sun Tsere Daga Wurin Zabe Bayan Sun Sha Bugu A Kogi

Jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC sun tsere tare da barin akwati mai lamba 001 a gundumar Asuta da ke karamar hukumar Kabba/Bunu ta jihar Lokoja bayan da suka sha mugun duka daga wadanda ake zargin ‘yan daba ne.

Jaridar The Cable ta samo wannan rahoton ne wajen karfe 2 na yamma, kafin fara kirga kuri’u. An samu rahoton lalata kuri’u a akwatuna da dama da ke kananan hukumomin Kabba/Bunu tare da Ijumu na jihar Kogi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *