Ma’aikatan jirgin kasan Najeriya sun dakatar da tafiya yajin aikin gargadi na kwanaki uku da suka fara domin neman a biya bukatunsu.
Dakatar da yajin aikin ya biyo bayan wani taro da aka yi da yammacin ranar Juma’a da hukumar NRC da kuma mahukunta da ma’aikatar sufuri ta tarayya a Abuja.
Sanarwar da aka fitar a karshen taron ta bayyana cewa an kafa wani kwamiti da zai fara aiki nan take kan sake duba yanayin aiki tare da wa’adin zuwa ranar 31 ga watan Janairun 2022.
Sanarwar ta samu amincewar Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikata jiragen kasa (SSA), kwamaret. Aliyu Mainasara da shugaban kungiyar ma’aikatan jirgin kasa ta Najeriya (NUR), Kwamared Innocent Ajiji, da daraktan gudanarwa na ma’aikatar, Dr. (Mrs) Monsurat O. Omotayo.
Taron ya kuma amince da cewa za a tattara bayanan ma’aikatan da suka mutu domin domin biyansu hakkin su nan take, kowane ma’aikaci yana cikin tsarin tabbatar rayuwa a kungiyar.
An kuma yanke shawarar cewa duk ma’aikatan jirgin za a ba su inshorar kamar yadda fasinjojin jirgin da kayayyaki da ke wucewa yayin da hukumar NRC da ma’aikatar sufuri ta dauki fifikon tsarin albashi a matsayin fifiko da nufin samun amincewa don aiwatarwa a cikin farkon lokaci mai zuwa.
Sanarwar ta kara da cewa, “An amince da cewa babu wani ma’aikaci da za a ci zarafinsa sakamakon shiga yajin aikin da ya yi na tsawon kwanaki 3 na masana’antu a watan Nuwamba 2021;
“Ta wannan sanarwar da shawarwarin da aka yi, an dakatar da yajin aikin kwanaki 3 na gargadin. Don haka, an umurci ma’aikata da su koma bakin aiki cikin gaggawa.”
Jaridar Dimukuradiyya ta rawaito cewa, yajin aikin da ya fara a ranar Alhamis ya gurgunta ayyukan jiragen kasa a fadin kasar inda aka dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa na Abuja-Kaduna da Legas-Ibadan da kuma Itakpe Warri.
Tun da farko, Manajan Darakta na NRC, injiniya Fidet Okhiria, ya yi kira ga ma’aikatan da su koma bakin aiki, yana mai cewa bukatun su na samun karbuwa.