Kungiyar masu kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya ta koka da rashin kyawun yanayin aiki tare da yin rashin daukar matakin hukumomi biyo bayan rasuwar abokin aikinsu Aniekan Effiong Inuk a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Kungiyar a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban kungiyar Abayomi Agoro da Sakatarenta Abayomi Agoro da Agbonlahor Felix suka sanyawa hannu a ranar Talata sun ce a cikin shekaru biyu da suka gabata, sun rasa mambobi 9 a hidimar aiki saboda matsalolin rashin lafiya da ke da nasaba da damuwa da alama suna da alaƙa da rashin yanayin aiki rashin isassun ma’aikata.
Kungiyar ta kuma ba da wa’adin makonni biyu daga ranar da aka fitar da takardar ga manema labarai da a magance bukatunsu idan ba haka ba “ba za mu iya ba da tabbacin daidaito da hukumomin ba.”
Sun kuma sanar da fara kula da zirga-zirgar jiragen na sa’o’i uku na tsawon kwanaki biyu don biyan bukatunsu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Kungiyar masu kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (NATCA) ta tashi daga wani taron gaggawa da aka gabatar game da rasa daya daga cikin masu ƙwazo, mai himma da nagarta, Mista Aniekan Effiong Inuk a safiyar ranar Litinin 22 ga watan Nuwamba, 2021.
“Korafe-korafe da yawa ga masu gudanarwa da sauran masu ruwa da tsaki a hukumar da rashin ayyukan da manajojin da suka dace suke yi game da sanarwar daga babban taron kungiyar na shekara-shekara da suka gabata sun kasa magance matsalolin.
“Mutuwar Mista Aniekan Effiong Inuk a bakin aiki a filin jirgin sama na Abuja wanda abun bakin ciki ne, kuma ba ya rasa nasaba da rashin samun motar da za ta kai shi asibiti a cikin lokaci da sauransu.
“Saboda haka, masu kula da zirga-zirgar jiragen sama suna shirin tsagaita zirga-zirgar jiragen sama na tsawon awanni uku (3) na tsawon kwanaki biyu, 23 da 24 ga Nuwamba, 2021 daga 0600UTC zuwa 0900UTC don yin rajistar rashin jin dadinmu tare da kira ga hukumomin da abun ya shafa da jama’a da su gaggauta magance mana matsalolinmu ba tare da bata lokaci ba. karin jinkiri,” cikin sanarwar ta fitar.