Kungiyar ma’aikatan shari’a ta kasar karkashin JUSUN sun tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani, don matsa wa gwamnati lambar ba su gashin kai.
A wata takarda da majiyarmu ta gani a ranar Asabar na karshen mako, ta ruwaito cewa yajin aikin zai fara ne daga 6 ga watan Afirilu, kuma a daukacin kasar.
Takardar da sakataren kungiyar I.M. Adetola ya rattaba wa hannu, ta bukaci membobin kungiyar da ke jihohi da ofisoshinsu su mutunta matakin da aka dauka.
Majiyarmu ta ce tuni aka fara rufe kotuna domin bin umurnin kungiyar. Inda bayanai suka nuna cewa a wasu kotunan ma wadansu da aka kai domin yi musu shari’a a Kano an koma da su gidan gyaran hali na Kurmawa sakamakon yajin aiki da ma’aikatan shari’a suka fara.
Ya kara da cewa hatta kotun daukaka kara ta Musulunci dake sakatariyar Audu Bako a jihar Kano, ita ma ta kasance a rufe.