By Ishaq Dabai
Don tabbatar da ingantacciyar Gomnati wacce take gina dukkannin tsare-tsaren ta bisa abun da al’uma suke bukata, yana da kyau Gomnati ta rika bayyanawa al’uma ayyukan da take yi.
Kamar yadda sauran Gomnatoci suke yi a karshen kowace shekara, Gomnatin jihar Yobe itama ta bi sahu wajen tara shuwagabanin dukkan ma’aikatu domin tattauna yadda aka tafiyar da kasafin shekarar data gabata da kuma yadda aka tsara tafiyar na shekara mai zuwa.
Sakataren Gomnatin jihar Yobe Alhaji Baba Malam Wali shine ya kaddamar da taron tattauna kudurin Kasafin kudin shekara ta 2022 wanda ya gudana a dakin taro na Ma’aikatar Kasafin jihar dake Birnin Damaturu.
Da yake jawabi, Shugaban taron wanda kuma shine Sakataren Gomnatin jihar Yobe Alhaji Baba Malam Wali, yace kason da ake samu daga Gomnatin Tarayya yana kankancewa ta yadda jihohi basa samun abun da zai wadace su, don haka akwai bukatar a fadada hanyoyin samar da kudaden shiga domin cike gibi.Ya kara da cewa Kasafin shekara ta 2022 zai fi bada fifiko ne wajen kammala dukkan ayyukan da aka soma.
Tun da farko da yake jawabin Kwamishinan Ma’aikatar Kasafin kudi na jihar Yobe, Alhaji Muhammad Abubakar Garba Gagiyo, yaja hankulan ma’aikatun jihar da su sanya bukatun jama’a a cikin kudurorin Kasafin su domin ciyar da jihar Yobe gaba. Sannan yace dole ne ma’aikatun jihar su dukafa wajen gano dukkan ayyukan da mutanen jihar suke so, da nufin gabatar da shi a cikin kudurorin Kasafi, domin yin hakan shine kadai mafita wadda zata baiwa Gomnati damar tafiyar da mulkin da kowa zai mora.
Shima a nasa jawabi, Shugaban Komitin kula da kudade da kasafi na Majalisar dokokin jihar Yobe, Hon. Chiroma A. Buba Mashio, yace Majalisar dokokin jiha tana iyaka kokarin ta wajen tabbatar da cewa anyi Kasafin da zai kyautata rayuwar al’uma.
Ya kuma bayyana cewa yanzu haka akwai kudurorin da ake saran mayar dasu doka a majalisa nan ba da jimawa ba, wanda zasu sake inganta Kasafin jihar domin daidaituwa da yanayin da ake ciki.