By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ma’aurata da dalibai biyu ne aka kashe a daren ranar Litinin a gasar tseren mota da wasu daliban jami’ar Ilorin ta jihar Kwara suka yi.
Jaridar Aminiya ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na dare a mahadar Ijalala dake cikin harabar jami’ar a lokacin da ma’auratan ke kan hanyarsu ta komawa gida.
Matar dai ba ma’aikaciyar jami’ar bace, ba ta koyar dasu daga sashin Sadarwa da Kimiyyar (CIS) na jami’ar wacce aka bayyana sunanta da Mrs Shakirat, yayin da aka ce mijinta ma’aikacin motar bas ne a cikin jami’ar.
Hadarin dai ya hada da wata mota kirar Toyota Lexus Saloon, motar bas da wata mota da wani dalibi a halin yanzu yake tukawa.
An dai bayyana cewa, Motar Toyota Lexus ta yi karo da motar bas din wanda ya yi sanadin mutuwar ma’auratan, direban Lexus da wani dalibi a ciki.
An ce wani mai yiwa kasa hudima na NYSC da wani dalibi a cikin motar bas din sun samu raunuka.
Sanarwar hadin gwiwa da shugaban da jami’in hulda da jama’a na kungiyar daliban jami’ar (SUG), Toafiq Waliu Opeyemi da Olabode Stephen Opeyemi suka fitar, sun bayyana cewa, abin takaicin ya faru ne sakamakon wuce gona da iri.
Jami’ar a cikin wata sanarwa da daraktan hulda da harkokin jami’ar Kunle Akogun, a cikin wata sanarwa, ta ce hukumar ta samu labarin cikin bakin ciki.
Sanarwar ta kara da cewa “A nan muna umurtar duk masu amfani da ababen hawa da su bi ka’idojin hanya, musamman yadda suka shafi iyakokin gudun.”