• About Us
  • Blog
  • Gwamnatin Jihar Kano ta ce ana gabda fara ginin masana’antun Iskar Gas a Jihar
  • Home
Tuesday, June 6, 2023
  • Login
Dimokuradiyya
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
Dimokuradiyya
No Result
View All Result
Home Labarai

Mabiyan Shaikh Zakzaky Aka Fi Zalunta Da Take Wa Hakki A Kasarnan, Inji Gamayyar Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adama

said by said
July 4, 2020
in Labarai
Reading Time: 2 mins read
0 0
0
1
SHARES
5
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil’adama da wasu kungiyoyin fararen hula na Arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, sun bayyana cewa Harkar Musulunci a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky sune mutanen da aka fi take wa hakkin cikin shekaru 40 da kafa Harkar fiye da kowanne mabiya a Nijeriya baki daya.

Gamayyar kungiyoyin sun bayyana hakan ne a yayin taron ‘yan jarida da suka kira a Otel din Bolingo dake birnin tarayya Abuja a yau Asabar 4 ga watan Yulin 2020 dangane da rashin tsaro da kuma take hakkin bil’adama a Nijeriya.

Kungiyar ta yi tilawar cewa daya daga cikin take hakkin da aka yi wa mabiya El-Zakzaky din ya hada da yadda rundunar sojan Nijeriya a karkashin jagorancin Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai suka yiwa mabiya El-Zakzaky din kisan kiyashi a cikin watan Disambar 2015; “Da sunan wai an tarewa Burutai hanya za a halaka shi, wanda hakan ya sanya sojojin suka kashe dubban marasa makami.” Inji kungiyar.

Gamayyar kungiyoyin sun nuna bacin ransu kan yadda rundunar sojin Nijeriya suka yiwa mabiya El-Zakzaky din kisan gilla; “tare da kona wasun su da ransu, yiwa wadansu fyade, rushe muhallansu, da kuma bizne daruruwansu a ramin bai daya. Tabbas ba za mu manta da wannan danyen aikin ba a ci gaba da fafutikar da muke yi wajen kare hakkin bil’adama a kasarnan.” Suka tabbatar.

Har wala yau a wani bangare na bayaninsu, sun bayyana cewa gwamnatin Nijeriya ta sabawa sashe na 33, 34, da kuma 36 na kundin tsarin mulkin 1999; “wanda ya ce kowanne dan Adam yana da ‘yancin rayuwa, kuma ba wanda za a hana ma wannan ‘yancin haka siddan. Kuma dole a hukunta wadanda aka samu wajen aikata wannan danyen aikin. Domin babu dan Nijeriya da ya dace a nuna wa wariya saboda abin da ya zabi ya yi, ko saboda kabilarsa, jinsinsa, muhallinsa, da kuma ra’ayin siyasarsa.” Suka lurantar.

Haka zalika kungiyar sun nuna yadda gwamnatin Nijeriya a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta nuna wa mabiya El-Zakzaky wariya da kiyayya. “Har wala yau an dakile musu ‘yancin bayyana ra’ayi akan kisan kiyashin Zariya idan aka yi duba da kwamitin binciken kisan kiyashin da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa, da kwamitin da fadar shugaban kasa da ta kafa kan take hakkin bil’adama da rundunar sojin Nijeriya ta yi.” Inji su.

Gamayyar kungiyar ta ce; mabiya Harkar Musulunci a Nijeriya, suna da ‘yancin gudanar da rayuwarsu da kuma mallakar wurare da ake ci gaba da rusa musu. “wanda a wani lokacin ma ake danne musu wannan hakki.”

A karshe gamayyar kungiyar sun yi kira ga gwamnatin Nijeriya da su bai wa kotun hukunta laifukan ta’addanci ta duniya, ICC hadin kai bisa laifukan da ake zargin Nijeriya da aikatawa da ya hada da na take hakkin ‘yancin bil’adama, tare da kamawa da kuma mika wa ICC dukkanin jami’an da suke da hannu wajen kisan kiyashin da aka yiwa ‘yan shi’a domin a yi musu hukunci.

Previous Post

Sama Da Kiristoci Dubu Takwas Boko Haram Ta Kashe A Adamawa -EYN

Next Post

Boko Haram Ta Hallaka Sojin Nijeriya 37 A Jihar Borno

Next Post

Boko Haram Ta Hallaka Sojin Nijeriya 37 A Jihar Borno

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result
  • Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    2602 shares
    Share 1041 Tweet 651
  • Batun Dakatar Da Opay Da Palmpay, CBN Ya Bayyana Gaskiyar Zance

    2343 shares
    Share 937 Tweet 586
  • Da Ɗumi-Ɗuminsa: Ƙazamin Rikici Ya Kaure Tsakanin Shugaban Ƙungiyar CAN Da Isa Ashiru Kudan

    2132 shares
    Share 853 Tweet 533
  • Sai na yi lalata da kai na kwanaki 4 babu ƙaƙƙautawa sannan zan taimaka maka, Wata mata ga saurayi

    1908 shares
    Share 763 Tweet 477
  • Ga Irinta Nan: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Ƙi Amsar Cikin Da Ya Ɗirka Mata

    1440 shares
    Share 576 Tweet 360
Da Dumi-Dumi: ICPC Ta Gano N258m Da Aka Boye A Ma’ajiyar Banki, Ta Kame Manajojin Bankin

ICPC Ta Gurfanar Da Wani Mutum A Gaban Kuliya Bisa Zargin Badakalar Ayyukan Yi

June 6, 2023
Majalisar Dattawa Ta Ki Amincewa Da Kudirin Dokar Albarkatun Ruwa

Majalisar Dattawa Ta Ki Amincewa Da Kudirin Dokar Albarkatun Ruwa

June 6, 2023
Taleko Ta Koma: Wani Gwamna Ya Dakatar Da Daukar Ma’aikatan Gwamnati

Taleko Ta Koma: Wani Gwamna Ya Dakatar Da Daukar Ma’aikatan Gwamnati

June 6, 2023
Gwamnan Jigawa Namadi Ya Yi Wasu Sabbin Nade-Nade

Gwamnan Jigawa Namadi Ya Yi Wasu Sabbin Nade-Nade

June 6, 2023
NEMA Ta Karbi ‘Yan Najeriya 109  Da Suka Dawo Daga Kasar Libya

NEMA Ta Karbi ‘Yan Najeriya 109 Da Suka Dawo Daga Kasar Libya

June 6, 2023
Kungiyoyin Turai Sun Shiga Zawarcin Messi

Kungiyoyin Turai Sun Shiga Zawarcin Messi

June 6, 2023
Da Dumi-Dumi: ICPC Ta Gano N258m Da Aka Boye A Ma’ajiyar Banki, Ta Kame Manajojin Bankin
Rikicin Duniya

ICPC Ta Gurfanar Da Wani Mutum A Gaban Kuliya Bisa Zargin Badakalar Ayyukan Yi

June 6, 2023
Majalisar Dattawa Ta Ki Amincewa Da Kudirin Dokar Albarkatun Ruwa
Labarai

Twitter

Archives

Recent Posts

  • ICPC Ta Gurfanar Da Wani Mutum A Gaban Kuliya Bisa Zargin Badakalar Ayyukan Yi
  • Majalisar Dattawa Ta Ki Amincewa Da Kudirin Dokar Albarkatun Ruwa
  • Taleko Ta Koma: Wani Gwamna Ya Dakatar Da Daukar Ma’aikatan Gwamnati

Quick Links

  • Tsaro
  • Siyasa
  • Labarai
  • Wasanni
  • Kasuwanci
  • Rikicin Duniya

Contact Us

info@dimokuradiyya.com.ng

0809 912 4425 +234 809 912 4425

No. 218 Mogadishu layout Kaduna City Center Ahmadu Bello way kaduna. Kaduna, Nigeria 800273

Copyright © 2023 Dimokuradiyya Media Services LTD.

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio

Copyright © 2023 Dimokuradiyya Media Services LTD.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In