Becky Hammon ta kafa tarihin zama mace ta farko da ta zama mai horas da fitacciyar kungiyar kwallon kwando a duniya, bayan da karbi mukamin a kungiyar San Antonio Spurs dake Amurka.
A bayan Hammon ce matakaimakiyar kocin kungiyar, sai dai bayan shan kaye da suka yi a hannun Los Angeles lakers da kwallaye 121 -107 a gasar kwallon kwandon Amurka, hukumar gudanarwar kungiyar ta kori Gregg Popovich dake horas da ‘yan wasanta.
Kafin darewa mukamin kocin, Becky Hammon ta shafe shekaru 13 tare da kungiyar kwallon kwandon ta San Antonio Spurs.