Dan wasan tsakiya na Belgium Youri Tielemans na daukar hankalin Real Madrid da Barcelona da Manchester United yayin da Leicester ke kokarin kulla sabon kwantiragi da dan wasan mai shekara 24. (AS)
Haka kuma Leicester din ta tuntubi kungiyar Sassuolo ta Serie A domin sayen dan wasan gabanta na gefe dan Italiya Domenico Berardi, mai shekara 27, a watan Janairu. (Leicester Mercury)
Ta bayyana cewa Barcelona ta yi tayin sake sayen Neymar mai shekara 29, fam miliyan 68 kafin matsalar rashin kudin da ta sa Lionel Messi barin kungiyar ya tafi Paris St-Germain. (Star)
Liverpool za ta nemi sayen dan wasan tsakiya na Valencia da Sifaniya Carlos Soler, mai shekara 24, a matsayin wanda zai maye gurbin dan Holland Georginio Wijnaldum, mai shekara 30, wanda ya tafi PSG. (Fichajes)
Dan wasan tsakiya na Manchester United da Faransa Paul Pogba na ganin ya kamata Ole Gunnar Solskjaer ya dauki dan wasan tsakiya na Monaco da ake kodawa dan Faransa Aurelien Tchouameni, mai shekara 21. (Express)
Kociyan Arsenal Mikel Arteta na jin dadi da farin ciki saboda Ainsley Maitland-Niles ya yarda ya tsaya a kungiyar, kuma ya bayyana cewa ya gana a asirce da dan wasan na Ingila mai shekara 22, wanda ya bayyana karara cewa yana son barin Gunners din a bazara. (Mirror)
Haka kuma Arteta ya ce dan wasan tsakiya na Ingila Jack Wilshere, mai shekara 29, na iya yin atisaye da tsohuwar kungiyarsa Arsenal yayin da yake kokarin samun wata kungiya bayan da Bournemouth ta sake shi. (Mirror)
Everton ta yi kokarin cimma yarjejeniyar sayar wa da kungiyar Istanbul Basaksehir ta Turkiyya dan wasanta na tsakiya James Rodriguez, mai shekara 30, amma kuma dan wasan na Colombia ya ki yarda ya bar Goodison Park. (AS)
Shugaban Barcelona Joan Laporta ya tabbatar cewa sun shirya ganawa da wakilan Ousmane Dembele, mai shekara 24, a kokarin da kungiyar ke yi na kulla sabuwar yarjejeniya da dan gaban na Faransa. (Fabrizio Romano)
AC Milan na sha’awar sayen dan wasan gaba na gefe na Real Madrid da Sifaniya Marco Asensio, mai shekara 25, a bazara mai zuwa. (TDFichajes)