Wani mafarauci ya kwanta dama bayan ya samu rauni daga harbin bindigar da karen sa yayi masa bisa tsautsayi lokacin da suke a cikin mota.
Mutumin wanda ya fito daga birnin Kansas, na ƙasar Amurka, karen sa ya bindige shi bisa tsautsayi yayin da suka fita farauta.
KU KARANTA KUMA: Ɗan wasan Manchester United ya samu mummunan Rauni, zai yi jinyar dogon lokaci
Rahoton jaridar Legit.ng ya tabbatar da cewa mutumin yana zaune a wajen tuƙi sannan karen sa na a kujerar baya lokacin da lamarin ya auku.
Rahoton ƴan sanda ya bayyana cewa sun fita farauta ne amma mutumin ya bar bindigar sa a baya inda karen nasa yake zaune.
A cewar rahoton ƴan sanda, mutumin mai shekara 32 a duniya ya mutu ne a ranar Asabar, 21 ga watan Janairu.
Rahoton yace karen na mafaraucin ya taka bindigar lokacin da take a kujerar baya, wanda hakan ya sanya harsashi ya fita ta saitin mafaraucin.
Mafaraucin ya samu mummunan rauni a cikin motat sa inda nan take yace ga garin ku nan.
An Kai Wani Mummunan Harin Ƙunar Bakin Wake a Wani Masallaci a Pakistan
A wani labarin na daban kuma, wani ɗan ƙunar baƙin wake ya kai mummunan hati a wani masallaci a Pakistan.
Wani ɗan ƙunar baƙin wake ya kai mummunan hari a wani masallaci a birnin Peshawar, a Arewa maso Yamma na ƙasar Pakistan.
Hukumomi sun bayyana cewa harin ya auku ne a ranar Litinin, 30 ga watan Janairun 2023, inda ya halaka aƙalla mutum 20 sannan sama da mutum 96 suka samu raunika.