Dan wasan gefe na Arsena Willian ya bayyana cewa watannin farko da ya shafe a Arsenal sun kasance mishi mafi muni lokaci a tarihin shi na kwallon kafa.
Willian ya hade da Arsenal ne a matsayin kyauta kan kwantirgain shekara uku inda farkon wasa shi karkashin koci Mikel Arteta kamar zai yi abin kirki bayan da ya fara da taimakawa a zura kwallaye biyu watan Satumba.
To sai dai daga bisani dakyar ya samu ya kara taimakawa aka ci kwallo guda cikin wasanni ashirin da hudu da ya na baya inda hakan ya sa Arteta ya fara yanke kauna kan dan wasan, amma bisa ga alama ya fara dawowa ganiyar shi bayan da ya bada kwallaye hudu aka ci cikin wasanni biyar da ya fafta a baya-bayan nan.
Da yake magana da Jaridar ESPN ta Kasar Brazil, Willian wanda shi ma dan kasar ta Brazil ne, ya ce “Babu ko shakka na ga haza a tun bayan kwallaye biyu da na bayar aka ci kan cikin kwallaye ukun da muka doke fulham”
“duk da cewa bayan wanchan wasan akwai wasanni da muka yi galaba kuma na yi kokari matuka, to amma daga bisani mun zo mun shiga wani mawuyacin hali”.
“Ni a kashin kai na, na fuskanci yanayi mai muni, zaqn iya cewa ma shine hali mafi muni da na taba shiga a tarihin kwallon kafa ta