Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya danganta matsalar tabarbarewar tsaro da ta zamewa al’umma kadangaren bakin tulu a Nijeriya da wasu kasashen Afrika, ga barayin gwamnati wadanda suka sace kudaden jama’a wajen karkatar da su zuwa ga ayyukan ta’addanci a kasashen da ke Afirkan wadanda ke fama da karancin ci gaba. Ya kara da cewa, biliyoyin Dala ne wadanda aka sata daga nahiyar tare da fita da su ketare ake amfani da su wajen rura wutar matsalar tsaro a Nijeriya da sauran wasu kasashen Afirka da dama, kuma suna hakan ne da nufin kara dakushe ci gaban nahiyar. Haka kuma, shugaba Buhari ya ce hanya kwaya daya wadda za a yi amfani da ita don taka wa wannan tabargaza birki ita ce, inda ya kalubalanci bangarorin tsaro a nahiyar Afrika, musamman kwararru a tona bayanan sirri, sai sun hada kai don tunkara da sa-ido wajen shige da ficen irin wadannan kudade da ake fita dasu ta barauniyar hanya. Muhammadu Buhari ya yi wannan furucin ne kwanakin baya a Abuja, kan yadda tabarbarewar tsaro ke kara kamari, sakamakon yadda wasu marasa kishin kasa ke dada rura wutar rikicin, saboda yadda suke amfana da ita; yayin da suke ci gaba da wannan karamar safara da kudaden haram. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabin bude taron kara wa juna sani, da kwamitin masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaro a kasashen nahiyar Afrika, inda shugaba Buhari ya tabo batutuwa dangane da ci gaban nahiyar Afrika da kalubalen da ya kewaye shi ta dalilin yadda wasu bata-gari ke sace dukiyar jama’a su tsallaka da ita, wadda ta doshi dalar Amurka biliyan 60, a kowace shekara. Jawabin na shugaban kasa Buhari an shi ne, ta hannun mai taimaka masa a sha’anin hulda da kafafen yada labarai, Mista Femi Adesina, ya bayyana cewa: “A zahiri, duk da bamu da cikakkiyar masaniyar illar da wannan matsalar ke haifar wa ba. Amma dai bisa wasu alkaluma suka nuna, kasashen Africa suna asarar sama da dalar Amurka biliyan 60, a kowace shekara, wadanda barayin gwamnati ke sace wa kuma su fita dasu waje, ta barauniyar hanya, makudan kudaden da ya dace ayi amfani dasu wajen bunkasa nahiyar”. “Haka kuma, fasa-kwaurin wadannan makudan kudaden, kamar yadda wani rahoton majalisar dinkin duniya ya nuna, irin matsalolin da fita da barayin gwamnati ke yi da kudaden sata zuwa kasashen waje; daga kasashen Africa, daga 1980 zuwa 2009,’ inda binciken ya gano a shekarar 1980 zuwa 2009- an tsallaka da kimanin dalar Amurka tiriliyan 1.2 zuwa $1.4 (daga Africa). Adadi mai matukar kima a ci gaban nahiyar Afrika”. In ji shi. Har wala yau kuma, shugaban kasa ya bayyana taken da aka sanya wa taron wannan shekara: “illar fasa-kwaurin kudaden sata daga Afrika da matsalar tabarbarewar tsaro da yadda yake sharar ci gaban kasashen’’, ya zo a lokacin da ake bukatar sa kana ankararwa ne ga masu ruwa da tsaki a sha’anin tattara bayanan tsaron kasashen Afrika 52, don sake daura damarar yaki da matsalolin da ke da alaka da lamarin a nahiyar”. A hannu guda kuma Buhari ya kalubalanci mahalarta taron kan akwai bukatar daukar ingantattun matakan da za su kai ga dakile duk wata kafar samun kudaden da yan ta’adda da masu aikata manyan laifuka ke amfani da ita, a miyagun ayyukan su. “Aikace-aikacen masu aikata manyan laifuka hadi da masu talkafa musu, suna mayar da hannun agogo baya a lamurran ci gaban nahiyar Afrika, ta hanyoyi daban-daban wadanda suke bi; sarrafa kudade ta haramtaciyar hanya. Yanayin da ya kai ba dare ba rana suna kokarin kirkiro da sabbin hanyoyin da suke amfani dasu wajen ci gaba da wannan bakar sana’ar fasa-kwaurin kudaden”. “Kuma a matsayin ku na kawayen juna kuma masu ruwa da tsaki a yaki da aikata manyan laifuka da matsalar tsaro, kun sani sarai kan yadda yan ta’adda tare da masu aikata manyan laifuka ke amfani da hanyoyi daban-daban, wajen hada hancin bata-gari da ke ta’amulli da miyagun kwayoyi, safarar makamai da na mutane da makamantan su, lamarin da ke rura wutar matsalar tsaro da fargaba a cikin wadannan kasashen”. Buhari ya kara da cewa, akwai bukatar amfani da ingantattun matakan dakile yaduwar matsalar, da karin haske kan cewa, “ta hanyar amfani da kowace fuska don aiwatar da bin doka da tsari, wajen ganin cin hanci da karbar rashawa basu sakata ba, hadi da fasa-kwaurin kudaden sata zuwa kasashen ketare, dole mu yi amfani dasu wajen ganin bayan su”. “Muhimmin aikin da na sa a gaba- a wannan kungiya ta kasashen Afrika ita ce yaki da cin klhanci da rashawa, lamarin da ya jawo mini farin-jini kana da ganin alfanun wannan kokarin a kasa, hadi da tashi tsaye wajen dakile fasa-kaurin kudaden da barayin gwamnati ke sace wa suna tsallaka wa dasu ketare- daga nahiyar Afrika”. “Saboda haka, ina mai tunatar da wannan taron kan cewa su yi gaggawa wajen kara fadada tunani, kan cewa lokaci ya yi wanda za mu hadu wuri guda tare da aikata abubuwan da muka dade muna tattauna su”. A gefe guda kuma, a nan Nijeriya, mun yi hobbasar tunkarar wannan kalubalen. Shi ne yadda muka daura aniyar ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa, don sake bunkasa ci gaban kasar mu. Kuma mun taka rawar gani, duk da har yanzu wasu barayin basu saduda ba, suna nan suna yunkurin bayar da hannun agogo baya”. In ji shi. Haka zalika kuma, shugaban kasa ya yaba da wannan kwamiti na CISSA, wanda aka kafa a Nijeriya a shekarar 2004 tare da yadda suke aiki babu kama hannun yaro wajen samar da bayanan sirri na tsaro cikin shekaru 15 da suka gabata, ya nuna cewa, kashin barayin gwamnati ya bushe nan gaba kadan- saboda ba abu ne mai wuya su samu kafar guje wa da irin wadannan kudi na haram. A nasa jawabin, shugaban wannan cibiya ta majalisar dinkin duniya, Musa Faki Mahamat, ya bayyana cewa aikace-aikacen kungiyoyin yan ta’adda wadanda ke samun tallafi daga irin wadannan kudade da ake safarar su daga Afrika zuwa kasashen ketare, suna ci gaba da shafar ci gaba da bunkasar nahiyar Afrika, yayin da su kuma yan siyasa ke rura wutar rikicin kabilanci da na Addini. Shugaban wanda Ambasada Smail Chergui, ya wakilta a wannan taron ya shaidar da cewa, wani zubi bata-garin su kan yi amfani da kafofin sada zumunta wajen zawarcin jama’a shiga ayyukan ta’addanci, sannan kuma yan ta’adda suna aiki da hanyoyin kimiyya ta zamani mai karfi wajen gudanar da aikin su. Haka kuma, Mista Mahamat, ya yaba wa gwamnatin shugaban kasa Buhari wajen kokarin sa na yaki da cin hanci da rashawa, wanda hakan ya taimaka wajen rage satar kudin al’ummar kasar.