•Alhaji Abdullahi Ya sauya sheka daga jam’iyar APGA zuwa jam’iyar APC.
• Ya sanar da sauya shekar ne, a wurin taron magoya bayan sa.
• Ya ce ya dauki wannan matakin ne domin cigaban jihar Zamfara.
Daga Shuaibu Ibrahim daga Gusau
A yau ne shugaban jam’iyar APGA kuma dan takarar gwamna ,Alhaji Abdullahi wamban shinkafi, ya bada sanarwar cewa, daga yau ya bar jam’iyar APGA zuwa jam’iyar APC.
Shinkafi ya bayyana hakan ne ga dubun dubatar magoya bayansa, a garin Gusau a yau Litinin, ya kara da cewa, ya yanke shawarar komawa wannan jam’iyar ce, sabida ganin yadda Gwamna Matawalle ya sauya alkiblan jihar Zamfara.
Ya kara da cewa, ba wani abu ya sa suka zabi wannan lokaci ba, sai domin ganin yadda jihar Zamfara take bukatar masu jajircewa, wadanda su ke da bukatar gina al’umar jihar Zamfara, ba aljihunan su ba.
Shinkafi ya bukaci magoya bayan sa, dasu kasance masu gaskiya da rikon amana, kamar yadda aka sansu, ya ce babu wanda aka tilasta masa na ya sauya sheka , inda ya ci gaba da cewa, wadanda suke da bukatar zama cikin jam’iyar APGA, suna iya zaunawa, babu wata matsala .
KARANTA WANNAN LABARIN: Ina Nan Daram a Jam’iyar PDP inji Kabiru Classic
Wamban na shinkafi ya bayyana wa magoya bayan nasa cewa, sun yi wannan wankan ne saka makon amsa kiran shugaban kasa Muhammad Buhari , ya ce ba suna wannan tafiya bane bisa ga gayyar sodi bane.” Inji shi.
Sai dai Abdullahi shinkafi ya ja hankalin magoya bayan jam’iyar APC cewa, “Ka da su yarda su biyewa wadanda suke so a durkusar da jihar Zamfara, don biyan bukatun kansu, ba tare da tunanin halin da jama’a suke ciki b”a.
Dukkan shuwagabannin jam’iyar ta APGA, na kananan hukumomi Goma sha hudu dake jihar Zamfara, sun fito daya bayan daya suna mika mubaya’arsu, da goyon bayansu ga shi jagoran tafiyar , Abdullahi wamban shinkafi.