Wani magidanci mai shekara 57 a duniya wanda ya fito daga jihar Kaduna yana neman ƙara aure inda zai auri mace ta biyu.
Shafin haɗa aure na Halal matchmaking a Twitter shine ya bayyana abubuwan da magidanci yake buƙata a wajen duk wacce ta shirya zata aure shi.
KU KARANTA KUMA: Yadda wasu yara masu ƙananan shekaru suka sace wata yarinya ƴar shekara 6
Magidancin kuma yana da kwalin digirin digir sannan ma’aikacin gwamnati ne, ƙwayun halittar sa AA, sannan jinin sa O+ ne.
Mutumin yana son mace matsakaiciya wacce ba tayi ƙiba sosai ba kuma ba tayi siririya ba, wacce take a tsakanin shekara 25 zuwa 35.
Yana kuma son wacce take da addini, tarbiyya da tsoron Allah. Sannan ya kuma yi nuni da cewa wacce ta haddace Al-Qur’ani na kan gaba-gaba.
Sharuɗɗan sa sun haɗa da zai biya sadaki daga dubu ɗari biyar zuwa abinda yayi sama, ba kayan ɗaki, ba zai yi lefe, ba zata zo da wani abu ba sai ita kaɗai sannan ba wani shagalin biki, musamman irin bidi’o’in da ake yi yanzu, amma za ayi walimah.
Shafin haɗa auren ya buƙaci duk ƴanmata da suke da ra’ayi da su tuntuɓe ta domin tantance su.
No lefe No kayan daki ( everything is well furnished ) And will pay N500 and Above for Dowry.
Any interested person should Dm me. pic.twitter.com/5QVOJ6c44z— Halal Matchmaking (@Halal_Match) January 11, 2023
An Samu Akasi: Kwalliyar Wata Amarya Ta Janyo Cece-Kuce
A wani labarin na daban kuma, wata amarya ta janyo kace-nace a dalilin irin kalar kwalliyar da aka yi mata a ranar auren ta.
Wata amarya ta janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta bayan bayyanar bidiyon ta wanda ya nuna irin kwalliyar da aka yi mata.
Mutane sun yi ta magana akan irin kwalliyar da aka yiwa amaryar saboda yadda aka cikata kuma ko kaɗan ba tayi kyau ba.
Sai dai ita amaryar ko a jikinta, domin samun ganin ta auri wanda take so ya fiye mata duk wani gutsiri tsoma da mutane za suyi ba, domin hakan bai sanya taji takaicin kwalliyar da aka yi mata ba.