Wani magidanci da ya ke son ya ba matarsa mamaki, sai ya zo da dubarar ya siya mata sabuwar waya.
Ganin cewa matarsa tana amfani wayar iPhone, amma wacce ta ke amfanin da ita ba ƴar yayi bace, sai ya yanke shawarar ya yi mata kyautar iPhone 14 promax, jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Hotuna sun bayyana yayin da Aliko Dangote ya ziyarci Bola Tinubu
Lokacin da ya shiga cikin gidan riƙe da kyautar, sai ya matar shi zaune a daƙi tana ɗauke da ɗan su.
Sai kawai ya miƙa mata wayar, ba tare da wani mamaki a fuskarta ba, sai ta miƙo hanni ta karɓa.
Bayan ta buɗe akwatin, sai ta yi arba da sabuwar iPhone ƴar yayi, sannan ta godewa mijin na ta a wulaƙance.
Ku kalli bidiyon a nan
Bidiyon ya sanya mutane da dama sun bayyana ra’ayoyin su a manhajar TikTok.
Ga kaɗan daga cikin waɗanda Dimokuraɗiyya ta tattaro:
@arewagodess ya rubuta:
“Kwata-kwata ba ta yi mamaki ba.”
@MelroseAniel ta rubuta:
“Sun saba da rayuwar girma shiyasa ba tayi mamaki ba.”
@lyeKamara ya rubura:
“Ni ki taimaka ki bani ɗayar wayar.”
@Louisa ta rubuta:
“Maganar gaskiya itace da yanzu wanna yaron yana ƙasa yayin da ni kuma da tuni ina kasuwa ina nunawa mutane cewa na yi waya.”
Wata Mata Ta Tona Asirin Masu Gidan Abincin Da Suka Amfani Da Kwashe-Kwashe, Bidiyon Ya Yadu
Wata ƴar Najeriya mai amfani da sunan @talk2veee a Twitter, ta caccaki wuraren siyar da abinci masu yin ɗan gwashe, onda ta yi mamakin cewa ko hakan yana ƙara mu su yawan ribar da suke samu ne.
@talk2veee ta yi tsokacin ne a Twitter lokacin da ta banƙaɗo wani abu da ta gano lokacin da ta je kai markaɗen tumatur da tattasai.