Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya ce magoya bayan Peter Obi hadari ne ga jam’iyyun PDP da APC.
Mabiyan dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar Labour Party ana kiransu da ”Yan gani kashe ni” “Obidients”.
A cikin wata makala tasa, Fani-Kayode ya ce yana da sha’awar sanin wanda suke marawa baya, da kuma wadanda suke wakilta.
KARANTA ANAN: Na Fita Daga NNPP — Shekarau Ya Zargi Kwankwaso Da Wulakantashi
Tsohon mai taimaka wa shugaban kasar ya lura cewa tasowarsu da kuma dacewarsu a siyasar Najeriya a cikin ‘yan makonni “abin mamaki”.
Fani-Kayode ya ce akwai bukatar mabiyan sauran jamiyyu masu rike da tuta a shekarar 2023 su fahimce su, su nemo yadda hankalinsu ke tafiya domin kayar da su a badi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ya kuma yi gargadin cewa zai kasance cikin hadari ga jam’iyyar APC da PDP su yi watsi da su.
“Gaskiyar magana ita ce, sun fi hatsari ga al’amuranmu na gama gari a matsayin masu mulki fiye da yadda da yawa daga cikinmu za su iya ɗauka ko kuma godiya,” Inji Fani Kayode.
A wani labarin kuma: Tilas Ne Yan Najeriya Su Zabi Tinubu a 2023 – Omisore
Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sen. Iyiola Omisore, a ranar Litinin, ya ce babu wani zabi ga yan Najeriya a zaben shugaban kasa, illa su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki Sanata Bola Tinubu.
Omisore ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da wasu shugabannin jam’iyyar a sakatariyar APC da ke Legas.