Daga: Abbas Yakubu Yaura
Magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour LP, Peter Obi, a ranar Lahadin sun gudanar da wani gangami a birnin kasuwanci na Onitsha na jihar Anambra, inda suka rufe galibin titunan birnin.
Matasan maza da mata da suka saka fararen rigunan polo masu dauke da hoton Obi da kuma rubutun jam’iyyarsa sun fara haduwa a Zik Avenue da misalin karfe 11:30 na safe, inda suka koma wasu sassan garin.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Sanda Sun Cafke Wani Kaftin Din Soji Na Bogi Mai Yiwa Mata Fashi
Kungiyar ta rike tutoci masu rubutu da dama wadanda ke goyon bayan Obi kuma sun yi tattaki cikin lumana a mafi yawan tituna, inda suka kare a filin wasa na Chinua Achebe, Fegge dake Onitsha.
Wanda ya shirya gangamin, Mista Chibuike Akpotue, wanda ya yi jawabi ga magoya bayansa ya ce: “Muna so mu nuna wa duniya cewa Obi yana da goyon bayanmu, an haife shi a Onitsha, ya taso a Onitsha, kasuwancinsa na nan. Don haka a yau muka yanke shawarar nuna masa hadin kai domin an ce mana ba shi da tsari, muna so mu fada musu mu ne tsarinsa.”
“Wannan ba batun jam’iyyar Labour ba ne, abu mafi muhimmanci shi ne muna son wanda zai canza tattalin arzikin kasar nan, tun da na kammala karatu ban sami wani aiki da zan yi ba sai na shiga kasuwanci, wanda hakan ba shi da dadi, a ra’ayin wani.
“Mun san adadin kudin da aka kashe wajen lodin mota daya a shekarar 2010 da kuma kudin da take kashewa a yanzu, mun san kudin da ake kashe mana wajen kula da iyalanmu kafin shekarar 2015 da kuma kudin da take kashe mana a yanzu, don haka babu kowa wanda zai iya cewa tattalin arzikin ya yi masa dadi.”
“Muna neman mutumin da zai iya juya tattalin arzikin kasar nan gaba ba jam’iyya ba. Ku duba tarihin Obi a matsayin gwamnan Anambra, za ku ga cewa shi kadai ne gwamna da ya yi shekara takwas amma bai taba samun wata matsala da EFCC ba kuma ya fita ba tare da wani rakiya ba.”
Kungiyoyin sun yi wa taron lakabi da, ‘Onitsha mega Rally: Uwar duk wata zanga-zanga’ ta haifar da cikas inda da yawan masu ababen hawa suka karkata zuwa wasu hanyoyi yayin da magoya bayan suke rera wa Obi yabo a lokacin doguwar tafiya.
A wani labarin kuma 2023: Bani Da Wani Dan Takara Dana Fi So, Cewar Obasanjo Bayan Ganawarsa Da Abdulsalami
Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ba shi da wani dan takara da ya fi so a zaben 2023.
An ga tsohon shugaban ne a wata ganawa da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da yayi a birnin Landan.