Wani mutum ya bayyana cewa da mahaifiyarsa ta san zai zama kafinta idan ya girma da ta tura shi cikin ruwa tun yana karami, Legit.ng ta ruwaito.
Saidai mutane da dama ba su ga aibin zama kafinta ba saboda sana’a ce mai daraja ba ta kaskanci ba.
KU KARANTA: Matashi ya kai wa budurwarsa ziyarar bazata, ya sha mamakin abin da ya gani
Kamar yadda yace, da kamar mahaifiyarsa ta san zai girma ya zama haka watakil da bata yi farinciki sosai kamar yadda tayi a lokacin ba.
A cewarsa, lokacin da ta haife shi ta yi murna kwarai, bata san zai girma ya zama kafinta ba a gaba.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake hira da wanda ya sanya shi aiki. Mutumin da yake daukarsa bidiyon ya dinga dariya a lokacin da yaji yana cewa:
“Lokacin da mahaifiyata ta haifeni ta yi farincikin haihuwar yaro, bata san cewa kafinta ya haifa ba.”
Ya cigaba da zolayar kansa inda yace mahaifiyarsa ta yi tunanin ta haifi likita ne ko lauya, kawai sai ga shi ya zama haka.
A cewarsa da ta san cewa zai zama kafinta idan ya girma da ta jefa shi cikin rafi kawai ta huta.
Mutane da dama basu kalli sana’ar a matsayin a wata ta kaskanci ba.
Shekarar da ta gabata warhaka muna shagalin aurenmu, Matashi na makokin rasuwar matarsa
Wani dan Najeriya mai suna Mustapha Ahmad Junaid ya koka bayan rasuwar matarsa Fatim Zarah, a ranar da ya kamata su cika shekara daya da aure, LIB ta ruwaito.
Zahra wacce ta rasu da juna biyu a ranar Laraba, 7 ga watan Satumban 2022, bayan watanni 8 da aurensu.
Mustapha ya auri Zahra ranar 26 ga watan Nuwamban 2021 a Jihar Sokoto. Ya yi wallafa a Twitter ranar 26 ga watan Nuwamban inda yace har yau yana fama da radadin mutuwar Zarah.