Yadda lissafin yake, a kallah mutane dari uku da goma (310) ne suka rasa rayukan su a kasar nan a cikin watan mayu a bangarori daban daban bisa ga kalubalen tsaro da suka hadar da masu garkuwa Yan bindiga da kuma hanyoyin masu kama da juna.
Mahaifar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, jihar Katsina, ita ce ta uku cikin Jihohi uku da ke gaba gaba dake fama da kalubalen rikice rikice, sauran biyu sun hadar da jihar Zamfara da kuma Borno, dake Arewa maso gabashin kasar nan.
Rahotan kididdigar binciken na kunshe cikin wani rahoto na musamman da wata kungiyar mai suna, Nigeria Mourns, ta fitar a babban birnin tarayya Abuja.
Kamar yadda kungiyar ta bayyana daga cikin mutane 310 da aka kashe a watan mayu a kasar nan 22 daga ciki Sojoji ne 7 kuma Yan-sanda ne.
Kungiyar Nigeria Mourns, ta ce 67 daga jihar Zamfara ne, 64 daga jihar Borno dake fama da kalubalen BokoHaram, yayin da a Jihar Katsina kuma jihar Shugaban kasa aka kashe guda hamsin daya.
Baya ga kashe kashe da manyan hare haren da Yan taadda da masu garkuwa da mutane da Yan BokoHaram da Yan sara suka suke kaiwa wanda shi ya jawo aka rasa rayukan mutane 310 bai hana fadar Shugaban kasa da sauran hukumomin tsaro ci gaba da ikirarin cewar an sami zaman lafiya ba, wanda hakan yasa Al’umma suka fara daukar matakin kariya, inji kungiyar
Baya da Borno da Zamfara da Katsina wasu Jihohin na fama da rikita rikitar rashin tsaro, Akwai jihar Jigawa da aka rasa mutane 26; da Lagos da Delta,Kogi, mutun daya 1 da Jihar Rivers mutane 18; a jihar Ogun kuma mutane 4 da Ebonyi da jihar Taraba, inda aka kashe mutane 29 da Plateau da kuma jihar Edo, mutane 12.