Rahotanni da suke fitowa daga birnin tarayya Abuja, sun nuna cewa; an saki diyar Dk Umar Ardo wanda aka sace a ranar Asabar da ta wuce a Abuja. Umar Ardo ya bayyana cewa sai da ya biya kudi masu yawa sannan aka saki Yarinyar.
Daily Trust ta labarto cewa wadanda su ka saci yarinyar, sun tuntube shi ne a safiyar Ranar Lahadi inda suka tabbatar masa da cewa za su sake ta idan har ya yi abin da su ke bukata. Ardo ya ce; ya amince ne bisa neman su yi masa alkawarin ba za su yiwa ‘yarsa komai ba ko ta hanyar kashe ta ko keta alfarmarta.
Tsohon ‘Dan takarar na PDP ya ce ya fada musu cewa idan har ba za su iya cika wadannan alkawura ba, to su tafi su je su yi duk abin da su ka ga dama da wannan Baiwar Allah. Wanda ke tsare da Yarinyar ya fada masa ta wayar salula da su ke zantawa cewa: “Dk na ga alamar cewa kai Dattijo ne, nima Dattijo ne. Na yi maka alkawarin ba za mu taba diyar ka ba.”
Umar Ardo ya ce daga nan ya tambaye su abin da su ke bukata, sai su ka fada masa cewa zai tura masu kudi Dala dubu 15 wanda kudin ya kama Naira miliyan sama da 5 da dubu dari hudu.
Masu garkuwan sun fada masa cewa idan ya saba za su kashe yarinyar. “Idan ba ka yi abin da mu ke so ba, ba za ka sake ganin ta da rai ba.”
Dan siyasar ya ce da yake wadannan mutane Dattawa ne, sun cika alkawarin da su ka yi, sun saki Budurwar babu kwarzane. Masu garkuwan sun nemi a biya wannan kudi ne da bitcoins inda ya fada masu bai san kan sa ba. A haka su ka koya masa yadda zai yi, ya kuma tura masu Dalolin daga asusun kudin kasar wajensa. Bayan dogon lokaci da aika masu wannan kudi, sai su ka sanar da shi cewa ya zo ya dauki diyarsa a wani wuri da ake kira Drumstick a Unguwar Gwarimpa, inda duka gidan su ka fita su ka ceto ta.