Alhaji Abubakar, mahaifin kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Hon. Nasiru Magarya ya mutu yayin da yake a tsare hannu masu garkuwa da mutane.
Mahaifin Kakakin wanda shine Hakimin kauyen Magarya, yan bindiga sun yi garkuwa da shi makonni takwas da suka gabata, tare da matarsa, da kuma jariri dan makonni uku da hai huwa.
Yayin da aka ceto wadanda aka sace a jiya Asabar, mahaifin kakakin Majalissar baya cikin su.
Kazalika da yake jawabi ga manema labarai, babban yayan mamacin, Malam Dahiru Magarya, wanda yana cikin wadanda aka sace ya ce, mahaifin kakakin Majalissar ya rasu ne a hannun Yan bindigan, sakamakon bugun zuciya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Kasurgumin Dan Bindiga ya shiga hannun Rundunar Yan sanda a Zamfara
Sai dai har kawo hada wannan rahoto majiyar Jaridar Do okuradiyya ta ruwaito cewa, Gwamnatin jihar da rundunar ‘yan sanda har yanzu ba su yi magana kan batun ba.
Kuma jaridar Puch ta ruwaito cewa, duk Kokarin da tayi na zantawa da kakakin majalisar abun ya ci tura, saboda an kasa samun lambobin wayarsa.