Rahotanni na nuni da cewa; Alhaji Musa Sale Kwankwaso, mahaifin tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa-Kwankwaso, kuma Hakimin Madobi ya rasu.
Hakan ya fito ne daga bakin Shaifullahi Hassan, mai taimakawa tsohon gwamnan kan Harkar yada labarai, inda ya ce mahaifin Kwankwason ya rasu ne da safiyar yau Juma’a yana da shekaru 93 a duniya.
Ana sa ran za a gudanar da jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada da misalin karfe 3 na ranar yau a Kano.