Basaraken garin Achi Mbieri a Ƙaramar Hukumar Mbaitoli ta Jahar Imo Eze Henry Madumere ya shaƙi iskar ƴanci, bayan shafe kwanaki biyar a hannun masu garkuwa da mutane.
Basaraken wanda shine mahaifin tsohon Mataimakin Gwamnan Jahar Eze Madumere, an sace shi a ranar Juma’a a Iho ta Ƙaramar Hukumar Ikeduru.
Yana dai akan hanyar sa ta zuwa gudanar da wasu ayyuka, a yayinda ƴan bindiga suka tare hanya tare da yin harbi a sama, kafin daga bisani su tafi dashi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Masu Fasahar Sadarwa Su Ne Suke Aikata Mafi Yawan Zamba A Banki– EFCC
Amma a ranar Laraba tsohon Mataimakin Gwamnan ya sanar dacewa mahaifin sa ya shaƙi iskar ƴanci, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa akan kafafen yaɗa labaru Uche Onwuchekwa ya fitar.
“Pa Madumere Wanda shine Mai riƙe da sarautar gargajiya a Ezi-Mbiera, masu garkuwa da mutane sun sako shi da sanyin safiyar ranar Laraba.
“An kuma nufi dashi kai tsaye zuwa Asibiti domin duba lafiyar sa, amma ya isa gidan sa dake Achi, Ezi Mbieri na Ƙaramar Hukumar Mbaitoli ta Jahar Imo.
Ya samu tarba daga ɗaruruwan mutane da iyalan sa da mabiyan sa cikin murna da annashuwa.