Daga: Abbas Yakubu Yaura
Mahaifiyar dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Sagbama/Ekeremor ta jihar Bayelsa a majalisar wakilai, Mista Fred Agbedi, ta rasu.
Madam Bebeapere Agbedi ta rasu tana da shekaru 111 aduniya a gidansu dake Yenagoa ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Yayin Da ‘Yan Sanda Suka Dakile Kai Wani Hari
Agbedi, dan asalin yankin Aghoro ne a karamar hukumar Ekeremor, ya sanar da rasuwar mahaifiyarsu a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Ya bayyana magidanciyar na dangin Agbedi a matsayin wani abin koyi na aiki tukuru da tarbiyya, mai kauna da kulawa da ‘ya’yanta da wadanda suka dauko.
Dan majalisar ya ce marigayiyar hazikar yar kasuwa ce, shugabar al’umma mai mutunci kuma kirista mai kishin kasa wanda ta yi aiki cikin kaskantar da kai da mutunci.
Ya yi nuni da cewa, duk da cewa mahaifiyarsu ta rasu ba ta samu damar yin karatun boko ba, amma ta kasance mai fafutukar neman ilimin kasashen yamma don samun ‘yanci.
“Ta horar da dukkan ‘ya’yanta don su samu shi (ilimi na yau da kullun) kuma ta yi wa’azi ga sauran ‘yan uwa, na kusa da na nesa don daukar sa da kuma ba da fifiko ga horar da yara,” in ji Agbedi.