By Abbas Yakubu Yaura
Tauraruwar Ace Nollywood Stella Damasus ta bayyana cewa mahaifiyarta ta rasu. Jarumar wadda ta yi bikin cika shekaru 11 da rasuwar mahaifinta a watan Janairun shekarar 2021, ba ta bayyana musabbabin mutuwar mahaifiyar ta taba.
Matar mai shekaru 43 ta sanar da rasuwar mahaifiyar ta a wani sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram a safiyar ranar Litinin. Ta raba hoton mahaifiyarta ta daukacin sashin inda ta rubuta, “Wannan ba bankwana ba ne, sai mun SAKE haduwa. Ina sonki har abada mahaifiya ta.”
Jim kadan bayan sanarwar, abokan aikinta a masana’antar nishadin sun shiga shafinta domin yiwa jarumar dake cikin jimami ta’aziyya.
Misali, abokin aikinta Andrea Chika Chukwu ya rubuta, “Ooh dear God. Kiyi hakuri sweety,ina addu’ar Allah ya jikanta da rahama, amin.”
Jarumar kuma tauraruwar Shaffy Bello a sauƙaƙe ta rubuta, cewa “Ina miki ta’aziyya masoyiya.”
Yayin da jaruma Halima Abubakar ta rubuta, “ kiyi hakuri ‘yar uwa.”
An haifi jarumar ne a ranar 24 ga watan Afrilun shekarar 1978. Baya ga wasan kwaikwayo, ta kasance mawakiya, An zabe ta a matsayin Jaruma mafi kyawu, sannan kuma a matsayin Jagora data lashe Kyautar Fina-Finan Afirka ta shekarar 2009.
Ta lashe lambar yabo ta gwarzuwar a (Nigeria Entertainment Awards) a shekarar 2007. A cikin shekarar 2012, ta sake lashe lambar yabo ta zinare mafi kyawun gwarzuwar jaruma a fim din Two Brides and a Baby a Houston dake Texas.