Rahotanni da suke fitowa daga jihar Katsina, sun bayyana cewa; mahajjatan jihar akalla 2, 000 ne suka dawo gida Nijeriya daga kasar Saudiyya. Alh. Ahmed Mohammed, shugaban kwamitin lura da aikin Hajji shi ne ya bayyana hakan a garin Katsina a ranar Asabar. Mohammed ya tabbatar da cewa; mahajjatan an dawo da su ne cikin tawaga hudu a kwanaki bakwai da suka gabata.
Ya kara da cewa; mahajjatan sun dawo cikin koshin lafiya da walwala da kwanciyar hankali. Ya ci gaba da cewa; suna jiran ragowar mahajjatan jihar 1, 000 da suka rage a kasa mai tsarkin cikin kwanaki kadan masu zuwa ta cikin jirgin Max Air wanda mamallakinta dan asalin jihar Katsina ne.
A karshe ya jinjinawa gwamnatin jihar bisa gudummawar da ta bai wa mahajjatan kafin tafiya da bayan zuwansa da dawowarsu.