Hukumar aikin Hajjin Nijeriya wato NAHCON ta bayyana cewa ya zuwa yanzu ta dawo da mahajjatan Nijeriya 31,435 zuwa gida cikin sahu 65 daga kasa mai tsarki. Cibiyar NAHCON dake Makkah ne ta bayyana hakan a ranar Alhamis, inda ta ce; mahajjatan da suka dawo na karshe sune mahajjatan jihar Kebbi har su 430 tare da jami’an NAHCON guda biyu a jirgin Flynas XY7484.
Haka zalika, sun ci gaba da cewa; akwai mahajjata 559 daga Borno da jami’in NAHCON guda a jirgin Max Air NGL 2080 wanda suka baro birnin Jeddah da safiyar ranar Alhamis agogon Saudiyya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa; hajjin bana na 2019, akalla maniyyata miliyan 1.8 suka sauke farali, a yayin da akwai mahajjatan Nijeirya dubu 65 a Saudiyya.