Kwana biyu da fara gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022 a kasar Qatar, da alama bakin da suka shiga kasar musamman daga kasashen turai suna kokarin kiyaye dokokin da kasar ta shimfida musamman ma na hana shan barasa a ko ina.
Ko da a kebantattun wuraren shakatawa na bakin teku da aka lamunce a iya hada hadar barasar, rahotanni sun nuna cewa mashayan sun tsorata, inda a zantawar Dimokuraɗiyya da Yakubu dogo, wanda ke aiki a wurin shakatawar yanzu haka a can birnin Doha, yace duk da wurin shakatawar zai iya daukar mutane 3000, kawo yanzu ko mutum 30 basu leka gurin ba.
KARANTA ANAN: Akwai Buƙatar Gaggauta Nazari Kan Ƙaruwar Yan Najeriya – Gbajabiamila
Dogo yace mahukunta a Qatar sun dauki matakan ba sani ba sabo kan duk wanda suka kama ya sha barasa kuma yana yawo a cikin gari.
Qasar dai ta dade tana gargadin masu yawon bude ido da zasu je don kallon wasan cin kofin duniya, kan abinda ka iya biyo bayan karya dokokin ta.
A wani labarin kuma: Gwamnatin Kano Zata Daina Tura Daliban Jihar Kasashen Waje Don Karatu
Gwamnatin Kano tace zata maida hankali wajen baiwa al’umma tallafin yin karatu a jami’o’in gida maimakon makarantun kasashen ketare.
Shugaban hukumar bada tallafin karatu na jihar Kano, Mudan Umar Bebeji, ne ya bayyana haka yayin kare kasafin kudin hukumar.
Ya ce kudin da za a kashewa yara guda 20 don yin karatu a kasashen waje ya isa a biyawa yara 500 suyi karatu a makarantu daban daban a kasar nan.