Mutum 20 ne suka rasa rayukansu yayin da aka sace mutane da dama a wasu hare hare biyu da aka a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a cewar Majalisar Dinkin Duniya .
Wadanda suka mutu sun hada da yara da akalla majiyyata hudu da aka kona da ransu a wani asibitin coci da ke lardin Kivu ta Arewa.
An dora alhakin harin kan mayakan kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) mai alaka da IS.
An bayyana kungiyar matsayin kungiya mafi muni masu dauke da makamai da ke aiki a kasar kuma Amurka ta ayyana ta a matsayin ‘yan ta’adda.
Shaidu sun ce ana ci gaba da gwabza kazamin fada a lardin Kivu ta Arewa mai fama da rikici inda sojojin Congo da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ke yin artabu da mayakan kungiyar.
Kafar yada labaran BBC ta ruwaito cewa, hare-haren na ‘yan tawayen sun fara ne a ranar Alhamis din da ta gabata a lokacin da ‘yan kungiyar dauke da makamai suka kai hari a wani asibiti a garin Lume inda suka kashe mutane da dama ciki har da majinyata hudu da aka kone da ransu a cibiyar lafiya.
Haka kuma tawagar Majalisar Dinkin Duniya a DR Congo ta ce daruruwan gidaje a kauyukan da ke kusa da su ma sun kone kurmus.
An ba da rahoton bacewar mutane da dama da suka hada da yara akalla 30 kuma ana kyautata zaton kungiyar ce tayi garkuwa dasu mutane da ba’a gamsu ba
Kazalika Dakarun wanzar da zaman lafiya sun kuma yi musayar wuta da mayakan a lardin Ituri.
A halin da ake ciki kuma, Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo mai arzikin ma’adinai na fuskantar sake barkewar rikici a baya-bayan nan da ya hada da kungiyoyi masu dauke da makamai da suka hada da kungiyar M23 da kuma Allied Democratic Forces.
A watan da ya gabata, shugabannin kungiyar kasashen gabashin Afirka sun amince da aike da dakaru a yankin da za su taimaka wa gwamnatin Kongo wajen dakile tashe-tashen hankula a gabashin kasar.